A tattaunawar da masanan suka yi ta cikin shirin gidan talabijin na Liberty mai suna “Democracy In Practice” a turance, sun bayyana ?aukar matakin hakan a matsayin abin da ya wajaba duba da irin halin da ?asa ta tsinci kanta a ciki.
Masanan wa?anda suka ha?a da babban sakatare na hukumar gidajen ya?a labarai ta Najeriya (BON) Dr Yemi Bamgbose, sai kuma Dr Emman Shehu daga cibiyar horar da ‘yan Jarida ta ?asa (IIJ) da Malam Sa’idu Carpenter ?wararren dan jarida.
Dr Yemi Bamgbose ya koka da irin halin da gidajen ya?a labarai suka tsinci kansu ciki a yanzu, inda ake gudanar da ayyuka bisa rashin kwarewa da sanin ya kamata, lamarin da ya jefa ?angaren cikin wani yanayi.
Ya kara da cewar halin da ?angaren gidajen ya?a labarai suka shiga, lamari ne mai matukar ha?ari, duba da yadda harkar ya?a labarai ta shafi komai na ?asar tun daga kan siyasa da tattalin arziki.
Kiran nasu na zuwa ne a dai-dai lokacin da kungiyar masu gidajen ya?a labarai masu zaman kansu ta Arewa (NBMOA) ta yi kiran gaggawa na gwamnati ta kawo wa ?angaren ?auki, duba da irin ?alubalen da gidajen ya?a labarai masu zaman kansu ke fuskanta a Najeriya.
A cikin wata budaddiyar wasika da suka aike wa shugaban ?asa Tinubu, Shugaban ?ungiyar masu gidajen ya?a labaran Alhaji (Dr) Ahmed Tijjani Ramalan, ya koka da yadda wasu gidajen ya?a labarai masu zaman kansu ke saka da mugun zare a ayyukansu, inda ya bada misali da tashar Arewa 24 wadda mallakin wata ?asa ce daga waje, sannan tashar ba ta da lasisi da hukumar kula da gidajen ya?a labarai ta ?asa, amma duk da haka tana aiki a Najeriya ?auke da sunan Arewa!

