Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya yi garga?in cewa jamiyyar APC mai mulki a Najeriya za ta fuskanci ?alubale a 2023 idan har shugaba Buhari ya kammala waadinsa.
Sanata Ahmad Lawan ya yi wannan garga?in ce a cikin jawabin da ya gabatar a taron matasan jamiyyar APC da aka gudanar a Abuja.
Ko mun ki mun so, gaskiya magana ita ce, goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari ne APC ta samu a sassan Najeriya, in ji shi.
Don haka ya ce dole ne jamiyyar ta fara tanadi da shiri domin samun ?orewar goyon bayan da ayyukan gwamnati mai ci ta hanyar tabbatar da shugabannin jamiyyar sun mi?a mulki ga matasan da suka cacanta na jamiyyar APC.
Shugaban majalisar dattawan ya ce Buhari na da rawar da zai taka ko da ya sauka amma kuma jamiyyar sai ta fi fuskantar babban ?alubale idan ya gama mulkinsa.

