Site icon Muryar 'Yanci

APC Ta Tsawaita Wa’adin Zabukan Fidda Gwani

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyya mai mulki, APC ta ?ara wa’adin ranakun za?ukan fidda-gwanin takarar gwamnoni, sanatoci, wakilan tarayya da na jihohi.

Sakataren Tsare-tsaren Jam’iyyar Suleiman Argungu ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Da fari an shirya za a yi zafin fidda-gwanin gwamnoni a ranar 18 Ga Mayu, shi kuma na Majalisar Jihohi a ranar 20 Ga Mayu, za a yi na Majalisar Tarayya a ranar 22 Ga Mayu, na Sanatoci kuwa a ranar 24 Ga Mayu.

Amma a yanzu sanarwar ta nuna za a yi za?en fidda-gwanin takarar gwamnoni a ranar 20 Ga Mayu, na Majalisar Dokokin Jihohi kuwa ranakun 22 Ga Mayu.

Za?ukan fidda-gwanin Sanatoci zai wakana ranar 24, sai kuma na Majalisar Tarayya kuma a ranar 25 Ga Mayu.

Exit mobile version