Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jamiyar APC mai mulki da kuma babbar jamiyar hamayya ta PDP ,sun mayar da martani ga tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo game da maganar da ya yi na cewa ya na kira ga matasan Najeriya da su goyi bayan ?an takarar shugaban ?asa na jamiyar Labour Peter Obi.
Kalaman dai na tsohon shugaban Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo ya yi, na cewa, ya na kira ga matasan Najeriya da su goyi bayan Peter Obi, bisa ga dukkan alamu bai yi wa manyan jamiyun biyu dadi ba.
Babban daraktan ya?a labarai da hul?a da jama’a na ?asa na jam’iyyar APC Bala Ibrahim ya shaida wa BBC cewa maganar Obasanjon ba wani abun damuwa ba ne domin ba wata magana ba ce sabuwa.
”Bana so in ?askantar da matsayin Obasanjo da martabarsa da darajarsa a matsayinsa na tsohon shugaban ?asa, amma gaskiyar magana ita ce Obasanjo ya zama mushen gizaka ne yara kawai yake bai wa tsoro, amma baya wani tasiri a abubuwan da yake yi” in ji Bala.
Ya ?ara da cewa Obasanjo ko akwatinsa ma baya kawowa, ballantana ?asa ba ki ?aya. Sannan kuma ya ce dama Obasanjon ya saba da irin wannan kira a baya kuma kiran nasa baya wani tasiri.
Daga nata ?angaren ita ma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta bakin Sanata Ibrahim Tsauri mamba a kwamitin dindindin na jam’iyyar ya ce tsohon shugaban ?asar na fama da gigin tsufa.

