Site icon Muryar 'Yanci

Ana Fama Da Karancin Kwaroron Roba A Kasar Kenya

Gwamnatin Kenya ta bu?aci ?an ?asar su yi amfani da wasu hanyoyi yayin da ake fama da ?arancin kwaroron roba.

An bayyana cewa ?asar na fama da ?arancin kwaroron roba, inda al?alumma suka nuna cewa kwaroron miliyan 1.6 gwamnati ta samar maimakon miliyan 455 da ya kamata a samar a shekara.

A cewar Star Kenya, wani rahoto da asusun ya?i da cutar AIDS da tarin fuka da maleriya ya nuna cewa kwaroron roba miliyan 20 aka raba a ?asar.

Jaridar ta ambato ma’aikatar lafiya ta ?asar na cewa gwamnati za ta yi ?o?arin magance matsalar fatarar ?waroron roba da ake yi a ?asar.

Lamarin dai ya haifar da muhawara musamman a kafofin sadarwa na intanet, saboda yadda wasu ke la’akari da manufar amfani da kwaroron roba domin kare cutuka da kuma hana ?aukar ciki.

Rahotanni dai sun nuna cewa an samu ?arancin ne sakamakon haraji da gwamnati ta saka wa kayayyaki.

Exit mobile version