Site icon Muryar 'Yanci

An Zargi Obasanjo Da Yunkurin Kifar Da Gwamnatin Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata Kungiya mai han?oron goyon bayan Shugaban ?asa Buhari mai suna ‘Buhari Media Organisation (BMO)’ ta zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da shirya makarkashiyar tumbuke Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga karagar mulki.

A wata sanarwa a ranar Lahadi, kungiyar ta ce wani “tsohon shugaban farar hula” da “gungun” wasu “makirai” ne suke kitsa wannan mummunan makircin, da ?o?arin haifar da kutungwilar kawar da Buhari daga madafun iko.

Ta ce masu shirya makarkashiyar da sunan ‘fitattun mutane’ sun shirya tayar da zaune tsaye don tilasta wa Shugaba Muhammadu Buhari sauka. Ko da yake kungiyar ta nisanci yin ishara kai tsaye zuwa ga Obasanjo, amma babu shakka akwai tunanin Obasanjo take nufi.

?ungiyar ta gargadi tsohon shugaban da abokan tafiyarsa da su hanzarta kawar da tunanin da kuma tseratar da kasar daga rikicin tsarin mulki da rikice-rikicen cikin gida.

Kungiyar ta magoya bayan Buhari ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi taka tsantsan da makiricin “fitattun mutane masu karfin iko da a shirye suke su jefa kasar cikin wani mummunan rikici da zai ci gaba da kasancewa barazana ga kasar.

Chief Obasanjo, daya daga cikin shugabannin farar hula biyu da ke raye, shi ne kadai zai iya tara ‘fitattun mutane’ don yin suka a kan shugabancin Buhari inji ?ungiyar.

A cikin shekarar 2018, Obasanjo ya yi kokari ya hada kan ‘yan siyasa don lalata sake zaben Buhari. Amma shirin ya faskara inji ?ungiyar.

Exit mobile version