Site icon Muryar 'Yanci

An Yi Nasarar Dam?e Maina

Jami’an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci sun kama Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai na PRNigeria ya ce an kama Maina a wani gari da ke cikin Jamhuriyar Nijar.

A cewar majiyar jaridar, an samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami’an tsaron Najeriya da Nijar.

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ne ta sanar da janye belin Abdulrasheed Maina tare da bayar da umarin a kama shi duk inda aka gan shi.

A hukuncin da alkalin kotun, Okong Abang, ya zartar ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, ya bayar da umarnin a sake kamo Maina ”duk inda aka gan shi”.

Lauyan hukumar EFCC, Mohammed Abubakar, ya ce an bayar da belin Maina a kan kudi miliyan N500 da kuma mai tsaya masa; wanda dole ya kasance Sanata mai ci da zai ajiye miliyan N500 a kotu.

Lauyan ya rubuta takardar korafi zuwa kotun inda a ciki ya zargi Maina da saba sharuda da ka’idojin belin.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa tuhuma goma sha biyu da ta shirya a kansa da kuma wani kamfani mai suna ‘Common Input Properties & Investment Limited”.

Bayan bawa hukumomin tsaro izinin kama shi, kotun ta bawa EFCC damar gurfanar da shi tare da tuhumarsa a kebance.

Kafin Sanata Ndume ya karbi belinsa, Maina ya shafe tsawon watanni bakwai a gidan yarin Kuje.

Bayan Maina ya cika bujensa da iska, kotu ta bayar da umarenin tsare Sanata Ndume a gidan yari na Kuje.

An rawaito cewa an hana wasu sanatoci damar ganin Ndume a gidan gyaran halin Kuje da ke Abuja.

An garkame Ndume ne a maimakon Maina, tsohon shugaban hukumar fansho da ake tuhuma da laifin wawura da sama da fadi da kudaden jama’a.

Da Sanata Na’Allah yaje ganin Ndume a gidsan gyarean hali, ya ce bai taba ganin irin wannan wulakancin ba a rayuwarsa.

Exit mobile version