Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Usman Alkali Baba, Sufeto-Janar na Yan sanda ya ba da umarnin aikawa tare da sauyawa mataimakan Sufeto-Janar na ‘Yan sanda 24 (AIGs) mukamai da kuma wuraren aiki na shiyyoyi.
A cewar wata sanarwa data fito a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, ta bakin kakakin rundunar yan sanda, CP Frank Mba, sauya wuraren aikin ya dace da sabuwar manufar ci gaban ‘Yan Sandan Najeriya.
Sanarwar ta nuna cewa AIG Bala Ciroma zai koma shiyya ta 7 Abuja yayin da AIG Usman Belel, AIG John Amadi da AIG Adeleke Adeyinka aka tura su zuwa FCID Annex Lagos, Maritime da shiyya ta 9 da ke Umuahia bi da bi.

