Rahotannin dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta girke ?arin jami’an tsaro domin tabbatar da komai ya tafi daidai gabanin ziyarar shugaba Buhari a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, shi ya tabbatar wa manema labarai hakan a Yola ranar Asabar.
Ya ce sun bukaci jami’an da su nuna ?warewa da kuma mutunta ‘yancin dan adam yayin gudanar da aiki.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Buhari zai ziyarci jihar ne a ranar Litinin domin kaddamar da ?akin neman za?en ‘yar takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Binani.
Kakakin ‘yan sandan ya ce ?arin jami’ai da girke sun ha?ar da rundunonin jami’an tsaro da jami’an sashin ?aki da ta’addanci da kuma motocin samame.

