Site icon Muryar 'Yanci

An Shiga Rudani Kan Takardun Makarantar Tinubu

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya shaidawa hukumar zabe mai zaman kanta cewa wasu mutane da bai sani ba suka sace masa takardun karatunsa lokacin da ya yi hijirar dole zuwa kasar waje.

Tsohon gwamnan na Jihar Legas, ya bayyana hakan cikin takardan rantsuwa da ya gabatarwa INEC yayin cike fom din takarar shugaban kasa cewa ya ‘tafi hijirar dole daga Oktoban 1994 zuwa Oktoban 1999 kuma da na dawo sai na gano wasu da ban sani ba sun sace kayayyakina har da takardan shaidan karatu da ake nema a sakin layi na 3.

A yayin da Tinubu ya tsallake bayanai na karatunsa na sakandare da frimare yayin cike fom din na INEC, ya ce ya yi karatu a Jami’ar Chicago tsakanin 1972 da 1976 inda ya yi digiri a bangaren Nazarin Tattalin Arzikin. Ya kuma ce yana da digiri a bangaren Kasuwanci da Gudanar da Mulki da kuma satifiket na aiki a matsayin Akanta.

Wasikar ta Tinubu, bisa alamu ta ci karo da bayanan da ya bayar a zaben da suka gabata a 1999, a lokacin da ya yi takara kuma ya ci zaben gwamnan Jihas Legas. Ya yi ikirarin ya yi karatun firmare da sakandare.

A lokacin, ya yi ikirarin ya yi karatun frimare a St Paul Children’s Home School, Ibadan, daga 1958 zuwa 1964; yayin da ya yi karatun sakandare a Government College Ibadan (GCI), daga 1965 zuwa 1968.

Ya yi ikirarin daga Ibadan ya kuma tafi Richard Daley College, Chicago, daga 1969 zuwa 1971. Sai dai, fitaccen lauyan Najeriya marigayi Gani Fawehinmi ya kallubalance takardun karatun yana mai cewa na bogi ne.

Exit mobile version