Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewar duba ga hauhawan matsalar rashin tsaro a jihar kungiyar shugabannin kirista a kudancin Kaduna sun kafa wani kwamitin mutum hudu don taron addua na wannan shekarar.
Tsawon shekaru biyu kenan ba a gudanar da taron adduan ba wanda aka saba yi duk shekara saboda annobar korona, da sauran kalubale na rashin tsaro.
Da yake rantsar da kwamitin a ranar Laraba a garin Kafanchan, jim kadan bayan taron mika masa shugabanci, shugaban kungiyar, Dr. Emmanuel Kure, ya bukaci mambobin kwamitin da su jajirce wajen ganin an cimma nasara a taron.
Ya bayyana taron adduan a matsayin mai muhimmanci, cewa za a yi adduoi domin dawo da yancin yankin da jiha dama kasa baki daya.

