Tsohon Sanatan Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani kuma ?an gwagwarmayar kwatar yanci ya bayyana cewa, sau ba adadi an yi masa barazanar kisa kawai don ya bayyana cewa, gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai tafi ko wace gwamnati sata a tarihin Jihar Kaduna..
Shehu Sani ya bayyana haka ne yayin wata hira da a ka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV a daren ranar Juma’a..
Haka zalika Sanata Shehu sani yayi rubuce-rubuce da dama akan irin satar da gwamnatin jihar Kaduna keyi a lokacin mulkin Malam Nasiru El-Rufai, a cewar Sani a baya ana masa kallon kamar adawa ce take saka shi furta irin kalaman cewa gwamnatin Malam Nasiru tayi sata sai gashi Gaskiya tayi halinta.

