Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayyar ?asar.
An yi bikin rantsarwar ne a gaban jami’an gwamnatin ?asar a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Laraba da safe.
Daga cikin wa?anda suka halarci rantsar da sabon sakataren gwamnatin sun ha?ar da mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima, da shugaban majalisar dattawan ?asar Sanata Ahmad Lawan da gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Dakta FolasadeYemi-Esan.
A makon da ya gabata ne sabon shugaban ?asar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da na?in George Akume da Femi Gbajabiamila a matsayin sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati

