Site icon Muryar 'Yanci

An Rage Ku?in Data A Najeriya – Pantami

Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar sadarwa ta rage kudin ‘Data’ da kashi 50% bisa umurnin da aka ba hukumar sadarwan Najeriya NCC.

Saboda haka, kudin ‘Data’ na 1GB ya sauko daga N1000 zuwa N487 daga yanzu .

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, wanda ya sanar da hakan ya ce, an yi hakan ne bisa umurnin da aka baiwa hukumar NCC na tabbatar da cewa an rage kudin ‘data’ a fadin tarayya.

“Haka yake kunshe cikin rahoton da hukumar sadarwan Najeriya NCC ta aikewa Minista bisa umurnin da ya bayar.”

Exit mobile version