Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya na?a tsohon ma’aikacin BBC Hausa, Balarabe Shehu Ilelah, a matsayin Babban Daraktan Hukumar Kula da Kafofin Ya?a Labarai ta National Broadcasting Commission (NBC).
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan Ya?a Labarai Lai Mohammed a yau Juma’a ta ce Balarabe Ilelah ya maye gurbin Armstrong Idachaba, wanda aka na?a ri?on ?warya a watan Fabarairun 2020.
Sanarwar ta ce sabon shugaban zai jagoranci hukumar na tsawon shekara biyar a matsayin wa’adin farko.
Babban aikin hukumar NBC shi ne sa ido da tantancewa da tabbatar da dokokin ya?a labarai masu sauti a Najeriya.
Balarabe Shehu Ilelah ya yi aiki da Sashen Hausa na BBC na tsawon lokaci kafin daga baya ya koma sashen Hausa na rediyon China (CRI).

