Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na?a wani mai bincike na musamman mai suna Jim Osayande da zai yi bincike a babban bankin Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaba Tinubu ya aika wa Obazee, shugaban hukumar masu bayar da rahotannin harkar ku?a?e ta Najeriya.
Tinubu ya ce za a binciki CBN da hukumomin da ke da ala?a da bankin ta hanyar amfani da ?wararru da hukumomin tsaro da masu ya?i da rashawa da suka dace don aiwatar da aikin.
Tinubu ya kuma aikewa Obazee kwafin umarninsa na dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Emefiele ke fuskantar shari’a kan zargin taimaka wa ta’addanci, sai dai ya musanta zargin.

