Site icon Muryar 'Yanci

An Kafa Dokar Kayyade Kayayyakin Aure A Jihar Jigawa

Rahotanni daga Jihar Jigawa na bayyana cewar Masarautar Gumel ta kafa sabbin dokoki kayyade kayan aure a yankinta domin saukakawa matasa aure sakamakon halin da al’umma ke fama da shi.

A takardar mai dauke da sa hannun Sakataren Masarautar kuma Maji Dadin Gumel, Alhaji Murtala Aliyu, an umurci Limaman Juma’a a Masarautar su fadakar da al’umma kan wannan sabuwar doka.

Masarautar tace ta kafa dokokin ne domin saukake wahalhalu da tsada da al’adu dake tattare da lamuran daurin aure.

A kwafin dokokin da masarautar ta hadawa Limaman, an ga jerin dokokin 19 da suka bayyana abubuwan da ya kamata Saurayi mai niyyar aure ya tanada.

Daga ciki Masarautar ta lissafa adadin abubuwan da mutum zai saya da kuma abubuwan da ba zai saya ba. Hakazalika an hana wasu tsare-tsare da bukukuwa da aka saba yi irinsu ranar Kauyawa da sauransu.

Exit mobile version