Mun samu labarin ‘?an bindigar da suka kai hari a jirgin ?asan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna sun harbi tsohon mataimakin Gwamnan jihar Zamfara H.E Mal. Ibrahim Wakala Liman, a kafa inda aka garzaya dashi zuwa wani asibiti a garin Kaduna domin ceto rayuwarsa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘?an bindigar sun dasa abin fashewa Bom ga jirgin mai ?auke da fasinjoji sama da 970 wanda suka yi nasarar tsaida jirgin bayan da sukai ta harbe harbe kan mai uwa da wani.
Lamarin ya faru tsakanin Katari zuwa Rijana kan hanyar Abuja.
Rahoton Jaridar Rariya

