A wani shahararren labari da kamfanin jaridar The Cable ta wallafa a yau, Jumaa, 15 Ga Yuli, ta bayyana wani rahoton bayanan sirri kan yadda gogarman Boko Haram, Kabiru Sokoto ya yi yun?urin sace ‘ya’yan Kashim Shettima a Abuja.
Kabiru Umar Sokoto ya yi wannan yun?urin ne wanda bai yi nasara ba a cikin watan Janairu, 2012, kamar yadda wasu bayanan tsaro na sirri su ka tabbatar. Ya nemi yin garkuwa da yaran ne lokacin da Shettima bai cika shekara ?aya da zama Gwamna Jihar Barno ba.
Kabiru Sokoto dai shi ne gogarman da ya shirya harin bama-baman da Boko Haram su ka kai a Cocin St Theresa Catholic Church, a Madalla, kusa da Zuba a Jihar Neja. An rasa rayuka a?alla 37 a harin, kuma mutane 57 sun ji munanan raunuka.
Da farko dai jami’an tsaro sun dam?e shi Gidan Saukar Gwamnan Jihar Barno da ke Asokoro, Abuja, a ranar 14 Ga Janairu, 2012, kafin a tsere daga hannun ‘yan sanda. An sake kama shi a Jihar Taraba bayan wata ?aya, daga can aka maida shi Abuja.
A cikin wata takardar bayanan tsaro ta sirri da aka rubuta ranar Alhamis, 14 Ga Yuni, 2012, wadda sai kwanan nan bayanan sirrin cikin takardar su ka bayyana, Kabiru Sokoto ya yi nasarar shiga Gidan Saukar Gwamnan Jihar Barno da ke Abuja ne da niyyar sace ‘ya’yan Gwamna na lokacin, Kashim Shettima, wanda dama bai da?e da ?auke yaran daga Maiduguri ba, ya maida su Abuja saboda dalilai na tsaro.
Takardar bayanan na sirrin wadda aka aika ta Fadar Shugaban ?asa, ta na ?auke da bayanin cewa kafin Kabiru ya nemi sace yaran a Abuja, an garga?i Shettima cewa Boko Haram na kitsa tuggun yadda za su yi garkuwa da ‘ya’yan sa domin su samu ma?udan ku?a?en biyan diyyar fansar yaran sa. Lokacin kuwa Shettima bai fi watanni takwas da zama Gwamnan Barno ba.
Shettima, wanda a yanzu shi ne ?an takarar mataimakin shugaban ?asa na jam’iyyar APC, sai ya yanke shawarar kwashe ‘ya’yan sa daga Maiduguri zuwa Abuja. Yaran wa?anda biyu mata ne ?aya kuma namiji, an maida wasu Turkish College a Wuse, ?aya kuma British School a Gwarimpa.
KABIRU YA YI SHIGAR BAREBARI:
Rahoton bayanan sirri wanda wani babban jami’in tsaro ya sa wa hannu, ya yi zargin cewa Kabiru Sokoto ya yi shiga sanye da kaya irin na mutumin Barno. Ta haka ne ya samu damar shiga Gidan Saukar Gwamnan Barno, inda ‘ya’yan Shettima ke zaune a lokacin.
An bada rahoton cewa ya sa?a?a ya shige cikin gidan a ?arshen mako, a ranar 14 Ga Janairu, 2012, lokacin da babu cinkoso da yawa.
A wani yanayi na keta dokar tsaro, Kabiru ya ro?i wani ba?on da aka rigaya aka saukar a gidan cewa ya bar shi ya kwana a gidan, saboda shi ma ba?o ne, ba shi da masauki.
Ba?on wanda ba a bayyana kowane ne ba a cikin takardar bayanan sirrin, sai Ahmed Sanda, wanda a lokacin shi ne Babban Sakataren Kula da Gidan Saukar Gwamnan Barno a Asokoro, ya amince ya yi kwana ?aya kacal.
YUN?URIN YIN GARKUWA A KAR?I FANSAR NAIRA BILIYAN 1
Bayanan sirrin sun nuna cewa Kabiru ya yi niyyar yin garkuwa da yaran a ranar Litinin, 16 Ga Janairu, 2012, kan hanyar su ta tafiya makaranta.
Jami’an ‘yan sanda sun dam?e shi bayan ya kwana a Gidan Saukar Gwamnan Barno.
Shettima ya maida yaran wa?anda a cikin su babu wanda ya kai shekara 10 a lokacin zuwa Abuja, a cikin Disamba 2011, wato makonni biyu kafin yun?urin yin garkuwa da su.
Ya ?auke su daga Maiduguri zuwa Abuja bisa shawarar jami’an tsaro, kuma bayan an dam?e Kabiru Sokoto, an ri?a danganta cewa ba a rasa kusanci tsakanin wasun su da Boko Haram. An ri?a kuma tunanin cewa su na sanar wa Boko Haram ?in bayanai a ?oye.
An ce Boko Haram sun ri?a shirya yadda za su yi garkuwa da yaran domin su kar?i naira biliyan 1, wadda a lokacin ku?in daidai su ke da dala miliyan 6.3.
JAMI’IN TSARO GUDA ?AYA KA?AI
Yaran sun bar gida Masaukin Gwamnan Barno zuwa makamata a ?ar?ashin kulawar antin su mata biyu, sai kuma wani kawun su ?aya, yayin da mahaifiyar su kuwa ta na yawan zuwa Maiduguri ta koma Abuja ne, saboda ta na zama ofishin ta na Matar Gwamna a Maiduguri.
Rahoton tsaro na sirri ya nuna cewa an yi sakacin yadda aka ha?a yaran da jami’in tsaro ?aya tal a kullum, wanda hakan ya sanya za su iya fa?awa tarkon masu garkuwa a sau?a?e.
Daga baya Shettima ya ?ara yawan jami’an tsaro a Gidan Gwamnatin Barno, sai ya ?auke yaran ya maida su makarantun kwana.
Wani babban jami’in tsaro da The Cable ta tuntu?a, ya ce ba shi da masaniya kan takarar bayanan sirri ta 2012, wadda ke ?unshe da bayanin yadda aka yi yun?urin yin garkuwa da yaran. Amma ya ce wannan zargin yun?urin yin garkuwa da yaran, ya yi daidai da irin yadda Boko Haram ke shirya sace wa?anda su ke yin garkuwa da su.
Daga baya Shettima ya zama mutumin da Boko Haram ke so su ga sun kashe shi.
“Ban san da wannan takardar bayanan sirrin yadda aka kama Kabiru Sokoto a Gidan Saukar Gwamnan Barno ba. Daga baya Kabiru ya arce yayin da aka tafi da shi a binciki gidan sa. An sake kama shi daga baya.” Inji jami’in tsaron.
“An gayyaci wasu jami’an kula da Gidan Saukar Gwamnan Barno domin a yi masu tambayoyi. Tabbas an yi bincike kan yun?urin ta’addanci a lokacin. Gaskiyar magana dai ba a same su da laifin komai ba. Kawai dai sakaci da aikin tsaro ne kawai, wanda ka?an ya rage da lamarin ya yi muni. Da an same su da laifi ko abin ya yi muni kuwa, to da an gurfanar da su a kotu.
“Tuna lokacin Shugaba Goodluck Jonathan, ai babu kyakkyawar ala?a tsakanin sa da Shettima. To da a ce a lokacin an samu wani laifi kan Shettima, to sai an fallasa shi ko a kai gulmar sa ga kafafen ya?a labarai. Tunda gwamnan jam’iyyar adawa ne a lokacin.
“Wato kawai dai lamari ne na sakarcin da har za a yi sakaci wani ya shiga Gidan Saukar Gwamna, kai ko da shi gwamnan ma ba ya ciki a lokacin.”
A ranar 20 Ga Disamba, 2013 Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke wa Kabiru Sokoto ?aurin rai-da-rai, saboda samun sa da laifin dasa bam a cocin Madalla.

