Site icon Muryar 'Yanci

An Gabatar Da Kudurin Karin Albashin Shugaban Kasa Da Mataimakin Sa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar tattarawa da raba ku?a?en shiga a Najeriya ta amince da ?udurin ?arin albashin za?a??un ‘yan siyasa ciki har da shugaban ?asa da mataimakinsa.

?udurin zai kuma shafi gwamnoni da mataimakansu da ‘yan majalisa da al?alai da sauran masu ri?e da mu?aman gwamnati.

Ta ce ?arin wanda aka yi a kan tsagwaron albashi (ban da alawus-alawus) ya kai kashi 114, abin da ke nufin shugaban ?asa zai iya kar?ar albashin da ya kusan kai naira miliyan biyu duk wata.

Shugaban hukumar (RMAFC) Muhammadu Shehu ya fa?a wa BBC cewa sun yi nazari bisa la’akari da halin da ake ciki a ?asa, kafin yin ?arin albashin.

Sai dai a cewarsa, matakin ?uduri ne kawai don kuwa sai an gabatar wa Majalisar Tarayya don amincewa kafin ya zama doka.

Haka zalika ?arin zai shafi ministoci da kwamishinoni da mataimaka na musamman kamar yadda sashe na 84 da sashe na 124 na tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

A cewar hukumar, karon ?arshe da aka yi wa za?a??un ‘yan siyasar ?arin albashi a Najeriya, shi ne shekara ta 2007.

Exit mobile version