Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Jihar Kaduna watau KASU ta dakatar da karatun ?alibai masu neman kammala karatun digirin farko har sai abin da hali ya yi.
Wata sanarwa da magatakan jami’ar KASU, Samuel Manshop, ya fitar ta ce daliban da ke karatun gaba da digiri da kuma fannin likita da na koyon harha?a maguguna da kuma wadanda ke karatun wucin gadi za su ci gaba da zuwa makaranta.
Wannan matakin na zuwa ne yayin da ake sukar gwamnatin Kaduna bisa matakin kara kudin karatu a jami’ar da kuma wasu makarantun gaba da sakandare a fadin jihar.
Gwamnatin Kaduna ta ?ara ku?in makarantar ne daga naira 25,000 zuwa tsakanin 150,000 da 250,000.
Galibin mutane na kallon matakin na Gwamna Nasir El-Rufai babu tausayi yayin da gwamnan ya ce yanayin tattalin arziki ne ya sa shi daukar matakin.
Daliban sun gudanar da zanga-zanga a makon da ya gabata domin jan hankalin gwamnati ta rage kudin saboda galibin ‘ya’yan talakawa ba za su iya biyan sabon kudin makarantar ba.

