Wani jaki ya sha?i iskar ?anci bayan da dakarun rundunar ?an sanda suka ku?utar da shi da ga hannun ?an fashin dajin da su ka yi garkuwa da shi a Jihar Katsina.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, Kakakin rundunar ?an sanda na Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da ku?utar da jakin, tare da sauran dabbobin gida da dama, a yayin da ya ke bayanin irin nasarar da rundunar ta samu a shekarar 2021 ga manema labarai a Katsina.
A cewar SP Isah, rundunar ta ?wato dabbobi 1, 243, inda yai bayanin cewa 867 da ga ciki shanu ne, tumaki 352, awaki 24 sai kuma shi wannan jaki guda 1.
Sannan SP Isah ya yi bayanin cewa ?an taaddan na amfani da jaki ne gurin tafiye-tafiye ko yin hijira zuwa dazuka, in da ya ce su na ?ora masa kaya, ?a?ansu da ma matan su a kai wajen yin bulaguro.
Ya ?ara da cewa jakin na mutanen gari ne, sai su ?an fashin dajin, idan sun zo satar dabbobi, sai su ha?a da jakuna domin su na amfani dasu.
Sun kama masu laifi har 999 a shekarar da ta gabata a jihar, sannan sun kama bindigogi da alburusai da dama.
Kakakin ya yi wa mutanen Katsina, da ma na ?asa baki ?aya albishir cewa a na sa ran a shekarar 2022 ?in nan, mutanen Katsina da ma?wabtanta za su ga ingancin tsaro sosai in Allah Ya yarda.
Ya ce gwamnatin taraiya za ta samar da sabbin kayan aiki, gami da ?aukar sabbin jamian ?an sanda, da kuma amfani da hanyoyin fasaha ta ya?i da ?an taadda, da dai sauransu.

