Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ofishin mai binciken kudi a gwamnatin tarayya ya sake aika wasu takardu zuwa ga Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa NPA, ya na zargin hukumar da rashin gaskiya wajen harka da kudi.
An ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta na zargin hukumar da yin aika-aika a shekarar 2018. Daga cikin zargin da ke kan wuyan shugabanninn Hukumar ta NPA akwai kin biyan hukumar FIRS harajin Naira biliyan 44.12 da yin facaka da Naira biliyan 88.23.
Akwai haka-haka a kan kudin da aka kashe a 2018 Rahoton ya ce Adolphus Aghughu ya na so hukumar da ke kula da tashoshin ruwan kasar ta yi masa bayanin inda ta kai wannan kudi a shekarar ta 2018 zamanin Shugabancin Hadiza Bala Usman.
Binciken da gwamnatin ta yi ya nuna cewa Hukumar NPA ta batar da Naira biliyan 409.17 da sunan sayen wasu kayan aiki, amma ba tare da an kawo takardun cinikin ba. Har ila yau, Mista Aghughu ya na zargin NPA da rashin kokari wajen karbo bashin da ta ke bi.
Hukumar za kuma ta yi wa gwamnatin tarayya bayanin yadda aka kashe kusan Naira biliyan biyu a yarjejeniyar gidajen da ta shiga da Aso Savings & Loans Plc.
An kashe N6.5bn wajen bada kwangiloli Shugabannin NPA sun ce sun biya Naira biliyan 6.5 domin ayi wata kwangila, wanda yanzu gwamnati ta bukaci a fito da bayanin wadanda aka ba kwangilar.
Rahoton ya ce gwamnati na bukatar sanin kamfanin da aka ba kwagila, yana yin kwangilar, kudin da aka ware, abin da aka fitar, da inda aka kwana a aikin a yanzu. An umarci NPA ta maida wasu Naira biliyan 2.33 a asusun gwamnati. An boye kudi ne a banki tun 2017 bayan EFCC ta shiga maganar wani sabani da aka samu.

