An ba wa kamfanonin sadarwa lasisin yin rajistar mutanen da ba su da Lambobin Shaidar zama dan Kasa don rage dumbin jamaa a ofisoshin Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa, in ji Hukumar NIMC.
Darakta-Janar na NIMC, Aliyu Aziz, ya ce wasu sauran kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati su ma hukumar ta ba su lasisi don samar da NINs domin magance cincirindon jamaa a ofisoshin hukumar.
Wannan ya zo ne yayin da maaikatan hukumar suka fada a ranar Talata cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami, ya kafa kwamiti don magance bukatun maaikatan NIMC.
Da yake amsa tambayoyi game da matakan da NIMC ta dauka dangane da korafin da yan kasa da kuma cincirindon jamaa a ofisoshin hukumar, Aziz ya ce an bai wa kamfanonin sadarwa na wayar salula ikon bayar da lambobin na ainihi.
“Mun ba da lasisi ga kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati da suka hada da telcos (kamfanonin sadarwa) don samar da wasu cibiyoyi,” kamar yadda ya bayyana a cikin sakon WhatsApp ga wakilin PRNigeria.

