Gwanatin Amurka ta yi wannan gargadi ne a yayin da Israila ke tunanin kai hari a matsayin martani kan harin ramuwar gayya da Iran ta kai mata a karshen mako.
Gwamnatin Biden ta bayyana karara cewa Amurka ba za ta sa hannu a hare-haren soji da Israila ke tunanin kaiwa Iran ba, saboda fargabar barkewar yaki a Gabas ta Tsakiya.
Wani babban jamiin kasar ya shaida wa yan jarida jim kadan bayan kawo karshen harin na Iran cewa Mun yi imanin Israila na da yancin ta kare kanta.
Amma da aka tambaye shi ko Amurka za ta taimaka wa Israila wajen tunkarar hare-haren soji, sai kaiwa ko, sai jamiin ya ce aa, Ba ba tunanin sanya kanmu cikin irin wannan abu.
A cewar wani jamiin kuma, Amurka ta riga ta isar da wannan sakon kai tsaye ga manyan jamian Israila a lokacin wata ganawar sirri ta wayar tarho ranar Lahadi tsakanin Sakataren Tsaro Lloyd Austin da Ministan Tsarnn Israila Yoav Gallant.
Jamiin ya ce Austin ya bayyana ?arara cewa Amurka ba ta shirin shiga wani hari da za a iya kaiwa a madadin Israila.
Wannan dai wani mataki ne da ba a saba gani Amurka ta dauka kan kawar tata ta kut-da-kut ba, wadda ta shafe gomman shekaru tana samun kariya da taimakon sojin Amurka fiye da kowace ?asa a duniya.
Wannan dai na zuwa ne bayan Israila ta kwashe watanni tana yin gaban kanta a kan Falas?inawa a yankin Zirin Gaza duk da irin kakkausar suka da take sha daga Amurka da sauran kawayenta cewa matakan sojin sun wuce gona da iri.
Harin da Iran ta kai kan Israila da yammacin ranar Asabar ya yi matukar kidima shugabannin duniya, ciki har da jamian Amurka.
Fadar White House ta ce da farko sun dauka cewa Iran na shirin harba wa Israila makamai masu linzami kadan ne kawai.
Wani babban jamiin Amurka ya bayyana cewa sun kadu a yayin da suka samu bayanai cewa jamian leken asirin Amurka sun yi imanin cewa Iran na shirya harba makamai masu linzami fiye da 100 ka Israila.
An dauki harin a matsayin ramuwar gayya ga harin da aka kai wani wuri da Iran ta kira karamin ofishin jakadancinta da ke birnin Damascus na kasar Syria, wanda ake kyautata zaton Israila ce ta kai harin.
A halin da ake ciki kuma, akalla makamai masu linzami na Iran guda tara ne suka yi barna a cikin Israila, biyu daga cikinsu a sansanonin sojin saman gwamnatin Israila.
Wani babban jamiin Amurka ya shaida wa ABC News cewa makamai masu linzami guda biyar na Iran kuma sun afka wa tashar jirgin soji Nevatim Air Base, inda suka lalata wani jirgin jigilar soji kirar C-130.
Ya kara da cewa wasu karin makamai masu linzami hudu sun afka wa sansanin sojin saman Negev, amma ya ce babu wani rahoto na gaggarumin barna da suka yi.

