Rahotanni daga birnin Washington DC na kasar A Amurka na bayyana cewar a ranar Talata, Sakataren ?asar Amurka, Antony J. Blinken, ya ziyarci Najeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually) inda ya gana da shugaba Buhari da kuma ministan kasashen waje, Geoffrey Onyeama.
Mutanen uku sun tattauna akan abubuwa da dama, wa?anda suka ha?a da; yadda zasu ha?a kai wajen ya?ar ta’addanci da rashin tsaro, gyaran ?angaren lafiya, bun?asa tattalin arzi?i da sauransu.
Hakanan kuma shugaba Buhari ya tattauna da sakataren kan yadda za’a bun?asa kasuwanci tsakanin ?asar Amurka da Najeriya, domin cimma biyan bukatun muradun karni a Najeriya.
Bayan wannan tattaunawar ne gwamnatin ?asar Amurka ta fidda bayani kan ala?ar dake tsakanin ?asashen biyu. A bayanin data fitar gwamnatin tace: “?asar data fi kowacce ?asa yawan jama’a, damokaradiyya, da kuma tattalin arzi?i a nahiyar Africa ita ce Najeriya, Najeriya tana ?aya daga cikin abokan mu masu muhimmanci a duniya.”
“Kasancewar shekarar 2020 tazo da ?alubale da yawa kuma ta aje tarihi, Najeriya ta fusaknci ?alubale da yawa a yayin da ?asar ke bikin cika shekaru 60 da samun yancin kai.” “Najeriya ita ce ?asar da aka fi samun mutanen dake zuwa ?asar Amurka daga Nahiyar Africa, inda akwai ‘yan asalin Najeriya 500,000 dake zaune a ?asar Amurka.”

