Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman da aka fi sani da Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sanaarsu, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura yayansu almajiranci.
Fati Slow ta ce tabbass babu asararre sama da mutumin da zai dunga iskanci yana watsawa duniya ana zagin iyayensa amma ko a jikinsa.
A wani bidiyo da ta saki a shafinta na Instagram inda a ciki ne ta yi shagube ga Nafisa, ta bayyana cewa jarumar bata da ilimin addini shi yasa har take iya kalubalantar tura yara almajiranci domin su koyo ilimin addininsu.
Naziru maganarka gaskiya ne babu cikakken dan iska kuma wanda iyayensa ma basu san yadda za su yi da shi ba shine wanda zai yi iskanci ya turo duniya ana ta zagin iyayenshi yana dariya, shine cikakken dan iska.
Kuma wanda yake ganin Naziru bai yi daidai ba, Naziru ya fito ya yi magana ka yi abun da za ka yi ko ki yi abun da za ki yi, ya fito ya fadi abun da ke ransa nima na fito na fadi abun da ke cikin raina.

