Rahoton dake shigo mana daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na bayyana cewar tsohon shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega yace wasu bara gurbin Alkalai su na cikin masu kawo cikas a kasar nan.
Farfesa Attahiru Jega yana cewa ana sa Alkalan kotu a harkar sauraron korafin zabe ne domin su samu hanyar da za su cika aljihunsu. A cewar babban malamin jamiar, wasu Alkalan su na saida shariar zabe, sai suyi wuf, suyi ritaya daga aiki domin gudun majalisar sharia ta kasa ta hukunta su.
Farfesa Jega ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya gabatar da watta lacca domin tunawa da Owolabi Afuye da kungiyar lauyoyi ta NBA ta shirya a Ibadan, jihar Oyo.
Tsohon shugaban jamiar ta Bayero da Kano, yace danyen aikin da Alkalai suke yi yana cikin abubuwan da ke haddasa rashin tsaro.
Wasu manyan lauyoyi sun yi kazamin kudi a dalilin kare jamian gwamnati marasa gaskiya a kotu, ko ta kare yan siyasa a shariar zaben gwamnoni da shugaban kasa.
Haka zalika Alkalai da-dama sun yi kaurin-suna wajen cin haram ta hanyar karbar kudi domin su saida sharia, musamman a shariar sauraron korafin zabe.
A baya ana zaben tsofaffin Alkalan da suka kusa yin ritaya a matsayin wadanda za su saurari karar zabe, su kuma sai su saida shariar ga wanda ya fi kudi. Sai su samu kudi, su yi maza su yi ritaya domin su kubuta daga hukuncin majalisar Shari’a.

