Hukumar EFCC tana zargin Bukola Saraki da laifin wawurar Naira biliyan 12 daga asusun gwamnatin jihar Kwara a lokacin da yake kujerar gwamna, ta hujjoji da dama.
?aya daga cikin shaidun da hukumar EFCC ta kawo ya bada shaida a gaban kotun tarayya da ke zama a Legas, ya fadi yadda Bukola Saraki ya yi facaka da dukiyar gwamnatin jiha.
Olamide Sadiq dake aiki da hukumar EFCC a matsayin mai bincike, ya shaida wa kotu cewa da kudin gwamnatin Kwara Saraki ya saye gidaje a garin Ikoyi.
Olamide Sadiq ya gabatar da wasu takardu dake nuna yadda tsohon gwamnan ya taba baitul-malin jihar Kwara. A cewar Sadiq, an dauki kudi daga asusun gwamnatin jihar Kwara, an zuba cikin wani asusun a daya daga cikin fitattun bankuna da Bukola Saraki ya mallaka.
Alkali mai sharia, Mohammed Liman ya saurari bayanin Sadiq, kamar yadda EFCC ta fitar da jawabi ta bakin mai magana da yawun bakinta, Wilson Uwujaren.
Gidajen da Bukola Saraki ya saya a Legas suna kan titin MacDonald ne a unguwar Ikoyi. Wadannan kadarori na tsohon gwamnan sun zama masa ala-ka-kai.
A cewar EFCC, Saraki ya wawuri kudin ne ta hannun wani daga cikin hadiminsa, Abdul Adama. Jamian hukumar EFCC sun buga alama a jikin gidajen tsohon shugaban majalisar dattawan.

