Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta bayar da umarnin ajiye Sanata Ali Ndume a gidan gyara hali Kurkuku.
Wannan hukuncin ya biyo bayan Sanatan batan Abdulrasheed Maina, wanda sanatan ya tsaya wa yayin karbar belin sa.
A zaman kotun na ranar Litinin, kotun ta umarci a kamo Ndume saboda rashin bayyana Maina wanda aka yanke wa hukunci a kan damfara.
Tun bayan bada belin maina ne aka fara wasar buya tsakanin kotun da shi Mainan inda ko a watannin baya sanata Ndume ya bayyana cewar shima ya kasa ganin maina duk da yasan wa’adin da kotu ta bada domin cigaba da sauraron karar yakai.

