Rundunar sojin Najeriya tace yanzu haka dalibai mata daga Sakandaren Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014, 98 ne ke tsare a hannun yan taaddan daga cikin 276 da suka kwashe.
Shugaban sashen kula da leken asiri na rundunar hadin kan dake yaki da yan taadda a arewa maso gabashin Najeriya da ake kira Operation Hadin Kai, Kanar Obinna Ezuipke ne, ya sanar da adadin ga manema labarai a Maiduguri.
Ezuipke yace daga cikin yan matan 276 da aka sace, 57 sun tsere daga hannun mayakan a shekarar 2014, yayin da aka saki 107 a shekarar 2018.
Shugaban leken asirin yace an ceto wasu karin yan mata guda 3 a shekarar 2019, guda 2 a shekarar 2021 sai kuma guda 9 a wannan shekara, abinda ya kawo adadin su zuwa 178.
Kanar Ezuipke yace suna samun gagarumar nasarar yakin da suke yi da yan taaddan a baya bayan nan, ganin yadda suka hallaka 43 daga cikin su, yayin da suka kama wasu 24 a watan Agusta kawai, bayan sama da 100 da suka hallaka a watan Satumba tare da kwato makaman da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda 129, da MG guda 3 da gurneti guda 17.

