Shugaba Bola Tinubu ya fara kamfen da taken sa na Renewed Hope Agenda, Ajandar Fatan Samun Sabon Canjin Rayuwa.
Ya fara kamfen wurjanjan a daidai lokacin da gwamnatin tsohon Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ta tsunduma yan Najeriya cikin ?uncin rayuwar matsalar sauya launin takardun Naira.
Wannan ya janyo mutane da dama sun ?agara mulkin Buhari ya ?are, domin ana ganin idan har Tinubu ya hau mulki, to zai iya yin amfani da ?udirorin sa na Renewed Hope Agenda, ya samar wa yan Najeriya sassaucin rayuwa.
To sai dai kuma maimakon haka, Renewed Hope Agenda ya fara da jefa Nejeriya cikin ra?a?in tsadar rayuwa, yayin da Shugaba Tinubu ya fara mulki da cire tallafin fetur, tun a wurin da aka rantsar da shi. Dama kuma ya ce ko da yan Najeriya za su yi kuka su gaji, to idan ya zama shugaban ?asa sai ya cire tallafin fetur.
Tun daga ranar da aka cire tallafin fetur ake fama da tsadar rayuwa a ?asar nan, kuma ba a san ranar fita daga wannan u?uba ba.
Tsadar fetur ta haifar da tsadar komai a Najeriya, har ma da hauhawar farashin Dala, inda sai da ta haura Naira 1,5000, yayin da litar fetur ta koma Naira 630. Yanzu kuma ?arancin fetur ya maida lita 1 zuwa Naira 1,050 a gidajen mai, kuma ya yi matu?ar wahala.
Tsadar abinci ta kai munin da sai da Gwamnatin Tarayya da Jihohi suka ri?a raba kayan tallafin abinci ga masara galihu.
Babbar matsalar da ake fuskanta ita ce yadda gwamnati ke gaggawar bijiro da tsare-tsare ko dokokin da za su takura jamaa, amma kuma ta ke jan-?afa wajen bijiro da tsare-tsaren da za su sau?a?a wa talakawa tsadar rayuwa.
An cire tallafin fetur a rana ?aya, amma kuma har yau dukkan tsare-tsaren da gwamnati ta ce za ta bijiro da su domin kawo sassauci, sai dabur-dabur da dawurwura ake yi a kan su. Ina banda rabon tallafin abinci da aka yi, wanda shi ma bai taka kara ya karya ba, sai dai ga mai jin yunwa ya kira abincin ci-kada-ka-mutu.
Ku?in fetur ya ?aru, ku?in ruwa ya ?aru, ku?in wuta ya ?aru. Ku?in shiga motar haya ya ?aru. Ku?in gina gida ya ?aru. Ku?in kama hayar gida ya ?aru. Ku?in kowane kayan abinci ya ?aru. Ku?in kayan masarufi ya ?aru. Ku?in makarantar yara ya karu. Ku?in sutura ya karu. Ku?in komai ya ?aru, amma kuma albashi na nan bai ?aru ba.
Matsalar wutar lantarki sai ?ara muni ta ke yi. Masu amfani da janareto wajen gudanar da sanaoi, a yanzu babu riba.
Jamaa sai rasa aikin su suke yi, ana sallamar su. Birkiloli da leburori babu aiki sosai.
A cikin wannan mawuyacin halin kuma yan taadda, mahara da yan bindiga masu garkuwa da mutane sai ?ara ?arfi su ke yi a Arewa.
Abin tambaya a nan shi ne, wane tasiri ko alfanu za a iya cewa ke tattare da Shirin Renewed Hope Agenda, shirin da a ?ar?ashin sa ruwan sanyi ma na yi wa talaka wahalar samu, a lokacin da yawancin gidaje ma abinci na gagarar magidanta da yayan su?

