Majalisar wakilai ta yi barazanar gayyatar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gurfana a gabanta saboda kin amsa gayyatar ta da tawa wasu maaikatansa suka yi.
Kwamitin dake kula da asusun ajiyar kudin gwamnati na majalisar ya ce shugabannin maaikatun CBN, NNPC, NPA sun ki amsa gayyatar da ta yi musu.
Ya ce akwai wasu harkar kudi ne da baa yi bisa kaida ba da kuma wasu ayyukan da na wasu maaikatun da wadanan hukumomi zasu amsa tambaya akai.
Shugaban Kwamitin, Wole Oke ya bayyana bacin ransa kan kin amsa gayyatar da wadannan shugabannin maaikatu suka yi, inda ya ce a aikewa shugaba a sanar da shi hakan dan ya tursasawa wadannan shugabannin maaikatu su gurfana a gaban makalisar.

