Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu jamian Hukumomin ya?i da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC sun bayyana cewa yanzu sun zama abin dariya, ba za a sake kallon su da daraja ba, ballantana a ?auki aikin su da muhimmanci, tunda Shugaba Muhammadu Buhari ya na yin afuwa ga gaggan ?arayin da suka kamo, bayan an ?ata shekaru masu yawa a kotu har aka ?aure su.
Da yawan jami’an wa?anda aka yi hirar da su a ?angaren EFCC da ICPC, sun ce, Buhari ya kashe mana jiki. Ba mu da sauran dukan ?irjin tabbacin samun nasara. Yanzu sai dai mu juri zuwa ofis aiki don kar?ar albashi kawai, amma babu sauran shau?in ya?i da cin hanci da rashawa a zuciyar mu.
Wa?annan kakkausan kalamai sun fito ne biyo bayan Shugaba Buhari ya yafe wa tsoffin gwamnoni biyu, Joshua Dariye na Filato da Jolly Nyame na Taraba.
Buhari ya yi masu afuwar ?aurin da Kotun ?oli ta jaddada a kan su, bisa dalili na tsufa da kuma rashin lafiya.
Buhari wanda ya hau mulki albarkacin romon-kunnen da ya yi wa yan Najeriya cewa zai ya?i cin hanci da rashawa, ya janyo wa kan sa tsangwamar da an da?e ba a yi masa irin ta ba, bayan ya yi afuwa ga manyan ?arayin da suka sace ku?a?en talakawan su.
Yanzu maimakon a ri?a jin tsoron mu saboda irin aikin da mu ke yi, za su koma ana yi mana dariya da gwalo, ana ganin ?ata lokacin mu kawai za mu ri?a yi, ko mun kamo mai laifi ma Buhari zai iya yi masa afuwa.
Abin da ya fi ba mu takaici shi ne yadda mu ke yin ba?in jini a wurin manya. Sannan a zo a yanke wa mutum hukuncin ?aurin shekaru, sannan a ce an yafe masa.
Dubi dai yadda aka ?ata kusan shekaru 10 ana je?ala-je?alar sharia a kotu. An kashe ku?a?e, an ?ata lokaci. Kuma abin mamaki fa wa?anda aka kama da laifin satar ce suka ri?a ?aukaka ?ara har zuwa Kotun ?oli, amma ba su yi nasara ba.
Mun sadaukar da rayukan mu, mun rasa abokan mu saboda yanayin aikin mu. Amma yanzu Buhari ya rushe mana gini.

