Site icon Muryar 'Yanci

Adamawa: Hukumar Zabe Ta Dage Zaben Kananan Hukumomi

Hukumar zabe mai zaman kanta a jahar Adamawa wato ADSIEC ta daga ranan zaben shuwagabanin kananan hukumomi ba kamar yadda ta aiyana tun farkoba wato ranan 27-11-2021 zuwa watan 12-2021.

Hukamar ta sanar da haka ne a wata sanarwa dauke da sanya hanun mai magana da yawun hukumar Daniel Zira.

Hukumar dai tace ta dauaki matakin canja ranan zaben ne biyo bayan taro da suka gudanar da wakilain jam iyun siyasar jahar karkashin jagorancin shugabar hukumar Mallam Isa Shetima.

Isa Shetima yace canja ranan zaben za baiwa jam iyun damar gudanar da aiyukansu yadda ya kamata.

A yanzu haka dai hukumar ta aiyana ranan 4-12-2021 shine sabon ranada za a gudanar da zaben shuwagabanin kananan hukumomi da kansiloli a dukkanin kananan hukumomi aahirin da daya dake fadin jahar Adamawa.

Exit mobile version