Site icon Muryar 'Yanci

Adamawa: Hukumar Zabe Ta Bada Wa’adin Kwanaki 90 Ga Jam’iyyun Siyasa

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta jahar Adamawa ta baiwa jam iyun siyasa dama masu ruwa da tsaki wa adin kwanaki casa in domin su shiya yin zaben shuwagananin kananan hukumomi dama kansiloli dake fadin jahar baki daya.

Shugaban hukumar zaben a jahar Adamawa Alhaji Isa Shetima ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a yola. Fadar gwamnatin jahar ta Adamawa.

Alhaji Isa Shetima yace sun dauki matakin bayan sun gudanar da taro da masu ruwa da tsaki dangane da lamarin. Wanda hakan yasa suka baiwa jam iyun siyasa wa adin kwanaki casa in domin su shirya Zaben kananan hukumomi ashirin da daya dake fadin jahar baki daya.

Isa Shetima yace hukumar ta dauki matakin haka ne bisa tsarin dokokin hukumar wanda ya baiwa hukumar damar gudanar da zabe
a fadin jahar baki daya.

Exit mobile version