A yayin da ake bikin ranan yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya N D L E A shiya ta biyu wanda ya ?unshi jihohin Adamawa Gombe da kuma Taraba tace ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi na dakile ayyukan shaye shaye a tsakanin Al umma.
Kwamandan hukumar na Shiyar Alhaji Idris Muhammed Bello ne ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu a ofishin hukumar dake Yola.
Idris Muhammed yace cikin nasarori da suka yi kawo yanzu sun kama miyagun kwayoyi da yawansu ya kai kilogiram sama da miliyan daya da mutane 428, 15 daga cikinsu Mata ne. Sai kuma wasu 324 wa?anda aka gyara musu halaye da kuma Mutane 82 wadanda aka yanke musu hukinci.
Kwamandan ya kara da cewa suna samun hadin kai da goyon baya daga gwamnatocin jihohin Adamawa Gombe da kuma Taraba.
Don haka nema yake kira ga iyaye da masu ruwa da tsaki da su bada tasu gudummuwa wajen yaki da hukumar take yi na hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a yankin, da kasa baki daya.
Ya kuma kirayi matasa da su nesanta kansu da tu’ammali da miyagun kwayoyi wanda a cewarsa tu’ammali da miyagun kwayoyi yana haddasa aikata laifuka daban daban.
Har wa yau kwamandan ya kirayi al’umma da su kasance suna taimakawa hukumar da bayanai da zai ba hukumar damar dakile matsalar ta shaye shaye a tsakanin al’umma baki daya.

