Site icon Muryar 'Yanci

Adamawa: Hukumar Kiyaye Hadura Ta Ja Hankalin Direbobi

A yayin da ake daf da gudanar da bukukuwan kirsimeti dana sabuwar shekara an kirayi matuka ababen hawa da matafiya da suyi taka tsantsan domin kaucewa haddura a yayin tafiya.

Kwamandan hukumar kare haddura da kasa F R S C shiyar jihar Adamawa Utten I Boyi ne yayi wannan kira a zantawarsa da muryar yanci a ofishin hukumar dake Yola.

Utten yace dolene su maida hankali wajen baiwa direbobi shawarwari duba da yadda ake lokaci na tafiye tafiye da kuma samun yawan karakainan motoci akan manya da kananan hanyoyi dake fadin kasan nan.

Don haka nema hukumar a jihar Adamawa ta dauki matakin baza Jami’anta akan hanyoyi dake fadin jihar a wani mataki na rigakafi domin ganin an samu nasaran kammala bukukuwan kirsimeti dana sabuwar shekara lafiya ba tare da matsalaba.

Boyi ya kara da cewa a yanzu haka suna hada kai da sauran hukumomin tsaro domin samun nasara da kuma cigaban aiyukansu yadda ya kamata. Tare da shawartan al umma da su baiwa hukumar hadin kai da goyon baya domin ganin hukumar ta cimma burinta na kare rayuka harm da dukiyoyin Al umma baki daya.

Utten ya kuma kirayi iyaye da su kula da yaransu a lokaci dama bayan bukukuwar na kirsimeti da sabuwar shekara da kuma kaucewa baiwa yara Mota wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen rage radadin haddura akan hanyoyi a fadin jihar ta Adamawa dama kasa baki daya.

Haddura akan hanyoyi dake fadin Najeriya dai kanyi sanadiyar asaran rayuka dama dukiyoyi masu yawa, lamarin da ake gani yana faruwane sakamokon rashin kyaun hanya ko kuma yawan gudu da direbobin keyi akan hayoyin ne ke haddasa hadduran.

Exit mobile version