An kirayi manoma da makiyaya da su kasance masu hada kansu da kuma kai zuciya nesa domin kaucewa tashin hankali a tsakanin manoma da makiyaya a fadin jahar Adamawa baki daya.
Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Aliyu Adamu ne yayi wannan kira alokacin yake tattaunawa da kungiyoyin manoma da makiyaya a yayinda ya ziyarci karamar hukumar Hong a jahar Adamawa.
Kwamishinan a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan yan sanda a jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje yace ya dauki matakin haka ne domin ganin ba a samu tashi hankaliba a tsakanin makiyaya da manoma.
Don haka nema ya shawarci manoma da makiyaya da koda yaushe su kasance masu neman zamàn lafiya domin samun cigaba a jahar dama kasa baki daya.
Shima a jawabinsa shugaban karamar hukumar Hong James Pukuma ya yabawa kwamishinan yan sadan bisa wannan majin kokari da yayi na hada kan manoma da makiyaya wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen Samar da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya.
Harwayau kwamishinan ya gargadi jami an tsaro dacewa duk wanda aka samu da hanu cikin duk wani karya dokan aiki to yayi kuka da kansa.

