Site icon Muryar 'Yanci

Adamawa: An Damke Matar Da Ta Yi Wa Mijinta Yankan Rago

Yanzu haka rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wata mai suna Rumasa u Muhammed yar shekara sha tara da haifuwa bisa zarginta da hallaka mijinta ta hanyar dafa masa wuka.

Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje wanda aka rarrabawa manema labarai a yola.

Rumasa u Muhammed ta dauki matakin hallaka mijin nata mai suna Muhammed Adamu dan shekara talatin da biyar da haifuwa biyo bayan ta bukaci da mijin nata ya saketa kuma yaki saketa wanda hakan yasa ta hallakashi.

Lamarin ya farune a kauyen Wuro Yanka dake cikin karamar hukumar Shelleng a jahar Adamawa wandama ofiahin hukumar yan sanda dake Shelleng din ne yayi nasaran kama matar da ake zargi da aika mijin nata lahira.

Tunin dai kwamishina yan sandan jahar Adamawa C P Aliyu Adamu ya bada umurnin gudanar da bincike kan lamarin kuma yace da zaran sun kammala bincike zasu gurfanar da ita gaban kotu domin ta fuskanci shariya.

Kwamishinan yan sandan yaja hankalin jama a da su daina daukan doka hanunsu. Duk wanda akayi masa ba daidaiba ya kaiwa hukumomin ko kuma wadanda lamarin ya ahafa.

Harwayau kwamishinan ya kirayi al umma da su cigaba da baiwa jami an tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin sun samu nasaran kawar da ta addanci a tsakanin al umma baki daya.

Exit mobile version