Site icon Muryar 'Yanci

Adamawa: An Bukaci Al’ummar Musulmi Su Hada Kai

An kirayi al umma musulmai a Najeriya da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin samun cigaban addinin musulunci yadda ya kamata.

Shugaban majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne yayi wannan kira a lokacinda yake gabatar da jawabin maraba a wurin taron kaddamar da kalandan addinin musulunci wanda majalisar addinin musuluncin jahar Adamawa ta shirya a yola.

Gambo jika yace hadin kai atsakanin al umma musulmai abune da yake da mutukan muhimmanci don haka akwai bukatan al umma musulmai su maida hankali wajen gudanar da aiyukan cigaban addinin musulunci dama hadin kan al umma baki daya.

Jika ya kuma shawarci al umma musulmai da su kasance masuyin amfani da kalandar addinin musulunci wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen hadin kai dama kawo karahen matsaloli da ake samu wajen duban wata.

Ya kuma kirayi iyaye da su maida hankali wajen nunawa yara muhimmancin kalandar ta addinin musulunci tare kuma da turasu makarantun addini da na zamani domin samun cigaban addini harma da zaman lafiya a tsakanin al umma musulmai dama sauran al umma Najeriya baki daya.

Harwayau Gambo Jika ya kirayi matasa da auma su shiga a dama da su wanda acewarsa addinin musulunci na alfahari da matasa a koda yaushe don haka akwai bukatan matasa su tashi tsaye wajen neman ilimi addini dana zamani domin bunkasa addinin musulunci yadda yakamata.

Shuwagabanin da dama da suka gabatar da jawabi a wurin tarondai duk sun maida hankali ne wajen Jan hankalin al umma musulmai ne kan hadin kai da kuma yin amfani da kalandar addinin musulunci.

Exit mobile version