Site icon Muryar 'Yanci

Adadin ‘Ya’yan Jam’iyyar APC Ya Haura Miliyan 41 – Mala Buni

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa adadin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki ya tashi daga Miliyan 11 zuwa Miliyan 41.

Buni, wanda shine shugaban jam’iyyar mai barin gado ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wajen taron gangamin jam’iyyar a Abuja.

Ya ce da yiwuwar adadin mambobin ya sake tashi daga milyan 41 saboda har yanzu ana rijista, wanda hakan ke nuna jam’iyyar ita ce sarauniya jam’iyyu.

Buni ya ce kwamitin rikon kwaryarsa ya samu nasarar sulhunta ?imbin ‘ya’yan jam’iyyar kuma ya janyo gwamnoni uku cikin jam’iyyar daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Gwamnonin sun hada da na jihohin Zamfara, Cross Rivers da Ebonyi, yayin da wasu ?arin gwamnonin ke shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar.

“A nasarorin da muka samu mun ra?awa sakatariyar APC sunan Buhari mun kammala aikin gyara hedkwatar jam’yyar kuma mun biya bashin kudin hayan da ake bin mu”.

Exit mobile version