Rahotanni daga Ofishin Hukumar EFCC dake birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ya warware kuma yana cikin koshin lafiya.
Abdulrasheed ya kasance cikin yanayi na jiri a lokacin gabatar da jawabi a wajen wani taro a fadar shugaban kasa.
Da fari jaridun Najeriya sun rawaito cewa yana bayyani ne kan wani mutum da aka kama da layukan waya 116 yana damfarar mutane, lokacin da ya soma jiri.
Jaridun sun kuma shaida cewa daga nan aka yi awon gaba da shi zuwa asibiti.
Ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami na cikin wadanda suka taimaka masa lokacin faruwar lamarin
EFCC dai bata yi karin haske kan abin da ya sa Bawa ya shiga yanayin rashin lafiya ba, a sanarwar da ta fitar

