Site icon Muryar 'Yanci

AbdulJabbar Bai Da Tabin Hankali – Cewar Asibitin Dawanau

Asibitin masu fama da matsalar kwakwalwa na Dawanau da ke jihar Kano ya ce Abduljabbar Kabara ba shi da matsalar kwakwalwa.

A ci gaba da zaman sauraren ?arar malamin da ake yi, duka lauyoyin Abduljabbar ba su halarci zaman kotun ba na ranar Alhamis.

Wakilin BBC da ya halarci zaman kotun ya ce lauyan Abduljabbar daya ne ya je kotun Barista Haruna Magashi kuma take ya ce ya janye daga wakiltar malamin.

Ya kuma ce “Sauran lauyoyin su ma sun janye daga kare Abduljabbar shi ya sa dukkansu babu wanda ya halarci zaman kotun.

A bayanin sakamakon gwajin asibitocin da aka gabatar wa kotun, Asibitin Dawanau na masu matsalar kwakwalwa ya ce an ta?a kwantar da Abduljabbar a asibitin na tsawon kwana hudu a baya.

“Lokacin da ya ta?a yin rikici da ‘yan uwansa an ta?a kwantar da shi a asibitin na kwana hudu, amma ba a ta?a yi masa gwaji ba kuma ba a ta?a ba shi magani ba,” in ji mai karanto bayani a gaban kotun.

Alkali Ibrahim Sarki Yola wanda ke yin shari’ar, ya tambayi sakamakon Asibitin Murtala da aka kai Abduljabbar domin yi masa gwajin kunne, saboda gaza amsa tambayoyin da aka yi masa a zaman kotun na baya, wanda ake tsammanin ko ya samu matsalar kunne ne.

“A sakamakon gwajin kunnen da muka samu daga Asibitin Murtala, an tabbatar da cewa Abduljabbar ba shi da matsalar kunne ko kuma ji ko ka?an,” mai gabatar da bayani ya ce.

Al?ali Yola ya ce ya amince da bu?atar lauyoyin Abduljabbar na janye wa daga kare malamin.

AbdulJabbarAn ?age sauraren ?arar Malamin zuwa ranar 30 ga watan Satumbar 2021

Exit mobile version