Site icon Muryar 'Yanci

A Kyale Inyamurai Su Kafa ?asar Biyafira – ?ungiyoyin Arewa

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya sun yi kira da babbar murya ga shugaban ?asa Buhari da cewar cikin gaggawa ya bada dama ga Inyamurai su kafa kasar da suke ta han?oro akai ta Biyafira domin zaman lafiyar Najeriya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa wadda ta samu sanya hannun mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin Abdul-Azeez Sulaiman kuma aka rarraba ta ga manema labarai.

Kungiyoyin Arewan sun cigaba da cewar tuni ba tun yau ba suka bayyana matsayin nasu na a amince Inyamurai su kafa kasar tasu ta Biyafira domin bayin Allan ‘yan Arewa su samu natsuwa da kwanciyar hankali daga farmakin da tsagerun Inyamurai ke kai musu a yankin Kudancin Najeriya.

Dangane da martanin da shugaban kasa ya mayar wa tsagerun na cewa zai yi maganin su nan bada dadewa ba, kungiyoyin Arewan sun ce kalaman Buhari akan wannan matsala abin takaici ne da ke nuna gazawa da raunin gwamnatin shi a fili.

“Ba tsoro ko fargaba bane ‘yan Arewa ke yi na kasar nan ta rabe, sai dai kawai natsalar da ake fuskanta a har kullum shine ?angaren manyanmu da ke ta kalaman ayi hakuri a zauna ?asa guda, wanda hakan ne ya haifar mana da raini har sashin Kudanci ke mana kallon ba a bakin komai muke ba suke barazanar a raba ?asa, wanda kowa ya san wanda zai ji jiki idan aka rabar ?asar”.

Saboda haka ya kamata shugabannin mu su gane cewar hanya guda ta kaucewa barkewar ya?in basasa a Najeriya shine abar Inyamurai su kafa kasar tasu ta Biyafira.

Kungiyoyin sun yi kira ga jama’ar Arewa da su zauna lafiya su kwantar hankalin su, sannan su goyi bayan Inyamurai su yi gaba su bar mana Najeriya su tafi Biyafirar su.

Sannan mun zuba ido mu ga matakin da shugaban kasa zai dauka nan da kwanaki 30 domin kawo karshen tataburzar da Kungiyoyin Inyamurai suke haddasawa a kasar nan a kusan kullum.

Exit mobile version