Site icon Muryar 'Yanci

A Gaggauta Binciko Dalilin Fa?uwar Jirgin Saman Dakarun Soji – Jingir

Rahotanni daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Babban Malamin Addini Islama Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi kira Shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukumomin rundunar Sojojin Najeriya dasu gagauta bincike domin gano hakikanin dalilin faruwar hatsarin jirgin saman Dakarun Soji.

Kiran Malamin ya biyo bayan yawaitar jita jita da ake ya?awa ne da cewar da akwai lauje cikin na?i a Hatsarin Jirgin Saman wanda ya yi sanadiyar mutuwar shugaban Dakarun Soji da wasu dakaru guda 10.

Hatsarin Jirgin Saman dai ya faru ne a Jihar Kaduna a lokacin da Jirgin shugaban Dakarun Sojin ke kan hanyarshi ta zuwa birnin Zazzau domin halartar bikin yaye daliban ?ananan Hafsoshin soja.

Tuni dai Hedikwatar tsaro ta bayyana cewar hatsarin jirgin ya samu ne dalilin rashin kyawon yanayi na sararin samaniya da aka samu.

Exit mobile version