?an takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyya mai mulki ta APC Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa zai cigaba da ayyukan Shugaba Buhari idan yayi nasara a shekarar 2023.
Tinubu ya bayyana hakan a jawabin da yayi na fatan alheri ga Buhari a taron bitar ayyukan Ministoci da Sakatarorin din-din-din dake gudana a babban birnin tarayya Abuja.
Ya ?ara da cewar idan ya ci zabe, ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an tarwatsa yan ta’adda a Najeriya da tabbatar da samun tsaro.
Ya yi wa Buhari alkawarin cewa zai karrama dukkan ayyukan da shugaban kasa yayi kuma ba zai watsa masa kasa a ido ba. Ya kara da cewa musamman zai kammala ayyukan gine-gine da gwamnatin Buhari ke yi.

