Site icon Muryar 'Yanci

2023: ‘Yan Najeriya Za Su Juya Wa PDP Baya – Garba Shehu

A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami’ar karya, wacce ta tara ma?aryata sannan ta cuci jama’a.

A cewar fada shugaban kasa, jam’iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa. Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta bayar da kwangilolin bogi, na karya, domin kawai a wawure kudaden jama’a.

Wani bangare na jawabin ya bayyana cewa; “cin hanci ne ya jawowa jam’iyyar PDP faduwa zabe a shekarar 2015, wanda dukkanin kasar an san da haka, kuma tabbas shi zai cigaba da yi wa jam’iyya llla.

“Ita kuwa gwamnatin APC a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta tsare kima mutuncinta. Ta samu nasarar murkushe cin hanci a fadar shugaban kasa, hakan ya sanya ‘yan Najeriya ke Allah san barka.

Jawabin ya bayyana cewa tasirin jam’iyyar PDP ya kare, mutuncinta tuni ya zube, Kuma ‘yan Nigeria ba zasu manta da irin ta’asar da suka tafka ba yayin mulkinsu.

Exit mobile version