Site icon Muryar 'Yanci

2023: Ya Zama Wajibi Shugabancin Najeriya Ya Koma Kudu – Gwamnonin Kudu

Gwamnonin kudancin Najeriya sun ce dole ne shugaban kasa ya fito daga kudancin kasar a zaben shekara ta 2023.

A wani taro da suka gudanar a jihar Enugu, gwamnonin sun jaddada wasu yarjejeniyoyi da suka cimma wanda Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, shugaban kungiyar gwamnonin ya ambato a wata sanarwa.

Yarjeniyoyin sun ha?a da bu?atar gwamnonin yankin ta ?an yankin ya zama shugaban Najeriya a 2023 da jaddada bu?atarsu ta shigar da gyaran da suke so a yi a kundin tsarin mulki da batun hana kiwo da batun harajin VAT.

Akeredolu ya ce “gaba ?aya gwamnonin yankin mun amince da cewa dole ne shugaban ?asa na gaba a Najeriya ya fito daga yankin Kudu. Sai dai kawo yanzu ba mu tsayar da mutum ?aya da zai fito a za?en 2023 ba.”

Kan batun hana kiwo, kungiyar gwamnonin ta ce ta gamsu da yadda jihohin kudancin Najeriya ke kawo gyara cikin dokokin kiwo a fili kuma Gwamna Akeredolu ya ce sun bu?aci sauran jihohin yankin da ba su sa dokokin hana kiwon, su yi hakan.

Haka kuma, ya ce jihohin yankin na da ?ancin kafa harajin VAT da ake samu daga jihohin da aka sayar, lamarin da ya janyo jayayya tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

Exit mobile version