Babbar Jamiyyar adawa a Najeriya PDP a taron masu ruwa da tsaki da ke gudanarwa a babban birnin Tarayya Abuja, ta sake duban matakin da ta ?auka a zaman ta na baya, inda a yanzu ta amince da cewa a zaben 2023 dake tafe, babu batun karba-karba.
Hakan, ya kawo ?arshen ra?e-ra?in da ake yawo da shi cewar ?an takaran shugaban ?asa na gaba zai fito ne daga yankin Kudu yayin da ?an takaran shugaban jamiyyar na ?asa ya fito daga Arewa.
Tun bayan zama da masu ruwa da tsaki na jamiyyar suka yi a kwanakin baya aka ta ya?a wannan batu, lamarin da ya tada hankalin magoya baan jamiyyar, yayin da magoya bayan jamiyyar APC mai mulki kuma suka samu abun fa?e.

